Deportivo za ta karbi bakuncin Barcelona

Image caption Barcelona tana mataki na daya a kan teburin La Liga

Barcelona za ta ziyarci Deportivo La Coruna a wasan mako na 34 a gasar La Liga a ranar Laraba.

A karawar farko da kungiyoyin biyu suka yi a Nou Camp a ranar Asabar 12 ga watan Disamba tashi wasa suka yi 2-2.

Barcelona wadda aka cire daga gasar cin kofin zakarun Turai ta bana, tana mataki na daya a kan teburin La Liga da maki 76.

Atletico Madrid wadda ke matsaayi na biyu a teburin tana da maki iri daya da na Barcelona, za kuma ta ziyarci Atletico Bilbao ne a ranar ta Laraba.

Real Madrid kuwa mai maki 75 a mataki na uku a teburin, za ta karbi bakuncin Villareal ne a Santiago Bernabeu.