Za mu iya wasanni babu Vardy - Fuchs

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Vardy ya ci kwallaye 22 a gasar Premier ta bana

Mai tsaron baya na Leicester City, Christian Fuchs, ya ce za su iya karasa buga gasar Premier ba tare da Jamie Vardy ba.

Vardy ba zai buga wasa daya ba, sakamakon korarsa da alkalin wasa ya yi a a wasan Premier da suka tashi 2-2 da West Ham United.

Watakila ma a tsawaita hukuncin, bayan da hukumar kwallon kafa ta Ingila ta tuhumi dan wasan da nuna halin rashin da'a lokacin da aka ba shi jan katin.

Vardy ya ci kwallaye 22 a gasar Premier ta wannan shekarar.

Sauran wasanni hudu suka rage a kammala gasar bana, kuma Leicester tana mataki na daya a kan teburin, inda ta bai wa Tottenham mai matsayi na biyu tazarar maki maki hudu.