Neuer ya tsawaita zamansa a Munich

Hakkin mallakar hoto Manuel Neuer Twitter
Image caption Manuel Neuer ya koma Munich ne a shekarar 2011

Mai tsaron ragar Bayern Munich, Manuel Neuer, ya saka hannu kan ci gaba da buga wa kungiyar tamaula zuwa shekara biyar masu zuwa.

Sai a shekarar 2019 yarjejeniyar Neuer wanda ya lashe kofin duniya da tawagar kwallon kafar Jamus za ta kare.

Mai tsaron ragar, mai shekara 30, ya lashe kofin Bundesliga uku da kofunan kalubalen kasar biyu da na zakarun Turai a Munich din.

Neuer ya koma Bayern ne da taka leda a shekarar 2011 daga Shalke 04.

Sauran 'yan wasan Bayern Munich da suka saka hannu kan ci gaba da wasa a kungiyar sun hada da Jerome Boateng da Thomas Muller da David Alaba da kuma Javi Martinez.