United za ta buga wasa da Crystal Palace

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Man United tana mataki na biyar a kan teburin Premier

Manchester United za ta karbi bakuncin Crystal Palace a kwantan wasan gasar Premier ta mako na 30 a ranar Laraba.

United ta lashe wasanni 10 da yin canjaras uku a karawar da ta yi da Crystal Palace a gasar Premier.

United din tana mataki na biyar a kan teburin Premier da maki 56, yayin da Crystal Palace ke matsayi na 16 da maki 39.

Liverpool ma za ta karbi bakuncin Everton a kwantan wasan mako na 27, West Ham kuwa da Watford za ta yi gumurzun kwantan wasan mako na 30.