Manchester United ta ci Crystal Palace 2-1

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption United za ta buga wasan gaba da Everton a gasar Premier

Manchester United ta samu maki uku a kan Crystal Palace, bayan da ta doke ta da ci 2-0 a kwantan wasan Premier da suka buga a Old Trafford.

Dan wasan Crystal Palace ne Delaney ya ci gida a minti na hudu da fara wasa, sannan Darmian ya ci ta biyu bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci.

United din tana nan a matakinta na biyar a kan teburin gasar Premier, inda ta rage tazarar maki daya ya rage tsakaninta da Arsenal mai matsayi ta hudu a teburin.

Manchester United za ta ziyarci Everton a wasan mako na 35 a ranar Asabar.

Liverpool kuwa doke Everton ta yi da ci 4-0, yayin da West Ham United ta ci Hull City 3-1 a kwantan wasannin Premier da suka fafata.