Real Madrid ta doke Villarreal da ci 3-0

Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Real Madrid tana matakinta na uku a kan teburin La Liga

Real Madrid ta ci Villarreal a wasan La Liga gasar mako ta 34 da suka fafata a Bernabeu ranar Laraba.

Madrid ta fara cin kwallo saura minti hudu a je hutun rabin lokaci ta hannun Karim Benzema.

Bayan da aka dawo ne daga hutun rabin lokaci Lucas Vazquez da kuma Luka Modric kowannensu ya ci kwallo dai-dai.

Madrid din tana matakinta na uku a kan teburin La Liga, bayan da Barcelona da Atletico Madrid masu maki iri daya 79, suka lashe wasannin da suka yi a ranar Laraba.