Premier: Arsenal ta doke West Brom 2-0

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kwallayen da Sanchez ya ci a Premier bana sun zama 12

Arsenal ta doke West Brom 2-0 a wasan Premier na mako na 34 inda ta ƙara ƙarfafa damarta ta kammala gasar cikin ƙungiyoyi hudu na farko, abin da zai ba ta damar buga gasar zakarun Turai.

Alexis Sanchez ne ya ci mata duka ƙwallayen biyu, inda ya jefa ta farko a raga minti shida da shiga fili sannan ya ƙara ta biyu a minti na 38.

Da wannan nasara yanzu Arsenal da maki 63 ta zama ta uku a tebur, da maki biyar tsakaninta da Tottenham wadda ke matsayi na biyu da maki 68.

Leicester City na nan a matsayinta na ɗaya da maki 73, yayin da Manchester City ke matsayi na huɗu da maki 61, ita kuwa Manchester United na matsayi na biyar da maki 59.