Ba na tsoron a kore ni — Martinez

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Roberto Martinez ya ce ba ya tsoron barin Everton.

Kociyan Everton Roberto Martinez ya ce ba ya tsoro a kore shi daga kulob din, yana mai cewa dole kulob din ya fuskanci kalubalen da ke gabansa.

Kulob din, wanda bai ci wasa bakwai na gasar Premier ba, ya sha kashi a hannun Liverpool da ci 4-0 ranar Laraba, sakamakon da Martinez a matsayin "mai matukar tayar da hankali".

Kulob din zai kara da Manchester United ranar Asabar a wasan kusa da karshe na cin kofin FA.

Martinez ya ce: "Za ka fuskanci suka da zarar ka sha kaye. Muna yin bakin kokarinmu, kuma bamu ji dadin yadda sakamakon wasanninmu ke kasancewa ba."

Martinez, mai shekara 42, na ci gaba da shan suka daga masu goyon bayan kulob din sakamakon rashin katabus dinsu.