An nada gawa a matsayin alkalin wasa

Image caption An nada Ibrahim Galadima domin yin sulhu a NFF.

Rikicin da ake yi a hukumar kwallon kafar Najeriya ya dauki sabon salo, inda aka yi zargin cewa an nada alkalin wasan da ya mutu domin yin alkalanci a wasan da za a yi tsakanin Warri Wolves da Giwa FC ranar Lahadi.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Chris Giwa ke ci gaba da cewa shi ne sahihin shugaban hukumar ta NFF, ba Amaju Pinnick ba.

Wata kotun Najeriya ta yanke hukuncin cewa Giwa ya maye gurbin Pinnick, wanda FIFA ke marawa baya, a shugabancin NFF, kuma tuni Giwa ya nada masu taimaka masa domin shugabancin hukumar.

A cikin mutanen da ya nada har da Wale Akinsanya, wanda ya mutu a watan Janairu.

Bangaren na Giwa ya aike da wasika kan nade-naden mukaman da ya yi ga shugaban hukumar lig ta Najeriya ranar Laraba.

Da alama dai dukkan bangarorin za su nada mutanen da za su wakilce su a wajen wasan da za a yi, lamarin da ka iya kawo hatsaniya.

Fifa ta fitar da wata sanarwar gargadi a makon jiya, inda ta ce dole a bar Pinnick ya ci gaba da shugabancin NFF, ko kuma a dakatar da Najeriya daga shiga harkokin wasanni.

A wani bangaren kuma, Giwa ya ki amincewa da kwamitin da ministan wasanni Solomon Dalung ya nada domin yin sulhu tsakanin bangarorin biyu.