Ronaldo ba zai buga wasan Vallecano ba

Hakkin mallakar hoto epa

Akwai yiwuwar dan wasan gaba na Real Madrid , Cristiano Ronaldo, ba zai buga wasan da kulob din zai yi da Rayo Vallecano ranar Asabar ba, bayan raunin da ya samu a cinyarsa ta dama.

Real Madrid ne na uku a saman tebirin gasar zakarun Turai, baya ga Barcelona da Athletico Madrid, ko da yake suna da ragowar wasa hudu a gabansu.

Kulob din bai sanar da lokacin da dan wasan zai koma murza leda ba, yana mai cewa " za a sa ido a kansa domin ganin yadda yake murmurewa".

Nan gaba Madrid zai kara da Manchester City, wanda shi ne wasan kusa da karshe a gasar cin kofin zakarun Turai ranar Talata.

Gareth Bale ya ci gaba da yin atisaye bayan jinyar da ya yi, lamarin da ya sa bai buga wasan da suka doke Villarreal da ci 3-0 ba.