Mace ta jagoranci maza lashe kofin Hong Kong

Hakkin mallakar hoto afc.com
Image caption Macen farko da ta horar da maza ta kuma lashe kofin Hong Kong

Chan Yuen-ting ta zamo macen farko da ta jagoranci maza a gasar kwallon kafa ta kwararru wajen lashe kofin Hong Kong.

Kulob din Eastern wanda aka kafa shekara 27 da suka wuce, ya lashe kofin gasar Premier Hong Kong, bayan da ya doke South China da ci 2-1 a ranar Asabar.

Chan, wadda ta karbi ragamar aikin horarwa daga Yeung Ching-kwong, a watan Disamba, ta lashe wasanni 14, inda aka doke su sau daya a karawa 15 da ta yi.

Eastern ya lashe kofin ne a karon farko a shekara 21 duk da saura wasa daya ya rage a kammala gasar bana.