UEFA na binciken Mamadou Sakho

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Liverpool za ta kara da Villarreal a gasar zakarun Turai

Hukumar kwallon kafar Turai, UEFA, na binciken dan kwallon Liverpool, Mamadou Sakho, kan shan kwaya mai kara kuzari.

Liverpool ta ce dan kwallon ba zai buga mata wasanni ba, tsawon lokacin binciken da ake yi, duk da hukumar kwallon kafa ta Turai ba ta dakatar da Sakho ba.

Mai yin sharhin labaran wasannin tamaula a BBC Radio 5, Ian Dennis, ya ce ana binciken dan kwallon ne a wasan da Liverpool ta ci Manchester United a ranar 17 ga watan Maris.

Dennis din ya kara da cewar an samu dan kwallon da laifin shan kwaya mai narka kitse, za kuma a sake auna shi a karo na biyu a ranar Talata.

Sakho wanda ya koma Ingila da murza leda daga Paris St-Germain a 2013, ya buga wa Liverpool wasanni 34, ciki har da guda 10 a gasar zakarun Turai ta Europa.