Everton zai yi fice nan gaba — Martinez

Image caption Martinez ya ce Everton zai yi fice nan dan lokaci masu zuwa

Koci Roberto Martinez ya ce Everton zai yi fice a nan gaba, bayan da yake shan suka kan yadda yake jan ragamar kulob din.

Kulob din Everon ya fice daga gasar cin kofin kalubale na Ingila a ranar Asabar, bayan da Manchester United ya doke shi da ci 2-1 a wasan daf da na karshe da suka kara a Wembley.

Rabon da Everton wanda ya lashe kofin FA sau biyar jumulla ya ci kofin tun wanda ya dauka a shekarar 1995.

Martinez na shan suka kan yadda yake jagorantar Eveton tun bayan da ya maye gurbin David Moyes a shekarar 2013.

Kociyan ya ce ya saba shan irin wannan sukar a kowace kakar wasa, amma Everton na renon matasan 'yan wasa da za su kai kulob din gaci a nan gaba.

Everton na matsayi na 11 a teburin Premier bana da kwantan wasa daya da maki 41.