Leicester ta bayar da tazarar maki takwas a Premier

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Leicester City tana da maki 76 a matasyi na daya a kan teburin Premier

Leicester City ta doke Swansea da ci 4-0 a gasar Premier wasan mako na 35 da suka kara ranar Lahadi a filin wasa na King Power.

Mahrez ne ya fara zura kwallo a minti na 10 da fara tamaula, Ulloa ya kara ta biyu saura minti 15 a tafi hutun rabin lokaci.

Bayan da aka dawo ne daga hutun Ulloh ya kara ta uku kuma ta biyu da ya ci a fafatawar, sannan Albrighton ya zura ta hudu a raga saura minti biyar ya raje a tashi daga wasan.

Leicester City ta ci gaba da zama a matsayi na daya a kan teburin Premier, ta kuma bai waTottenham wadda ke mataki na biyu tazarar maki takwas.

Leicester za ta buga sauran wasaninta uku da Manchester United a Old Trafoord, sannan ta karbi bakuncin Everton, ta kuma yi wasan karshe a gasar da Chelsea a Stamford Bridge.