Muna cikin matukar damuwa — Wenger

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wenger ya ce rashin nasararsu abin takaici ne sosai.

Kociyan Arsenal Arsene Wenger ya ce yana cikin matukar damuwa saboda akwai yiwuwar ba za su yi nasarar zuwa gasar cin kofin Zakarun Turai ba a bana, karon farko cikin shekara 19.

Kulob din Arsenal ya kasa samun damar zama na uku a kan tebirin Premier bayan sun tashi 0-0 a karawar da suka yi da Sunderland ranar Lahadi.

Wenger ya ce, "Mun damu sosai da kasancewarmu na hudu. Abin takaici ne, saboda muna yin wasa ne domin mu lashe kofi, don haka rashin nasararmu abin takaici ne sosai".

Kulob din Arsenal, wanda bai taba fita daga cikin jerin kulob hudu na saman tebirin Premier ba tun daga kakar wasa ta 1995-96 ba, yanzu yana bayan Leicester da maki 12, inda yake da ragowar wasa uku da zai buga.