Toure ba zai buga wasa da Real Madrid ba

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Manchester City za ta karbi bakuncin Real Madrid a Ettihad

Watakila Yaya Toure ba zai buga wa Manchester City wasan gasar cin kofin zakarun Turai da za ta yi da Real Madrid a ranar Talata ba, sakamakon raunin da ya yi.

Toure ya ji rauni ne a karawar da City ta ci Stoke City 4-0 a gasar Premier a ranar Asabar, duk da haka bai bar filin wasan ba, saboda kungiyar ta gama sauya 'yan wasan da doka ta amince.

Sai dai kuma kyaftin din City, Vincent Kompany, wanda ya buga wa kungiyar wasanni 20 a bana ya ce ya murmure daga jinyar da ya yi.

Real Madrid za ta ziyarci Ettihad a ranar Talata tare da dukkan 'yan wasanta, inda Madrid din ke fatan Ronaldo da Benzema su samu sauki kafin karawar.