An ci kwallaye 266 a gasar Firimiyar Nigeria

Hakkin mallakar hoto NPFL Twitter
Image caption An kammala gasar mako na 13 a gasar Firimiyar Nigeria

Kwallaye 266 aka zura a raga a gasar Firimiyar Nigeria, bayan da aka kammala wasanni 123 a karshen makon nan.

A kuma karshen makon ne aka yi wasanni 10 inda aka ci kwallaye 25 a raga.

Kano Pillars ce ta zura kwallaye 6-0 a ragar Shooting Stars, kuma Emmanuel Edmund ne ya ci uku rigis a karawar.

Enyimba ce ta samu nasara da ci daya mai ban haushi a gidan Akwa United, shi ne wasan da wata kungiya daga waje ta lashe wasa a gasar ta mako na 13.