Juventus ta lashe kofin Serie A

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Juventus ta lashe kofin Serie A na 32 jumulla

Juventus ta lashe kofin Serie A na Italiya na bana kuma na biyar a jere, bayan da Roma ta ci Napoli daya mai ban haushi a wasan mako na 35 da suka kara ranar Litinin.

Juventus din ta hada maki 85 daga wasanni 35 da ta yi, inda ta ci 27, aka doke ta 4 ta yi canjaras 4 ta kuma zura kwallaye 67, inda aka ci ta 18.

Napoli wadda ke mataki na biyu ta yi nasara a hannun Roma ta buga wasanni 35 ta lashe 22 ta yi canjaras a wasanni 7, aka doke ta sau 6 inda take da maki 73.

Sauran wasanni uku suka rage a kammala gasar bana, inda HiguaĆ­n na Napoli ke gaba a yawan cin kwallaye inda ya ci 30 a gasar.

Jumulla Juventus ta dauki kofin Serie A sau 32, sai AC Milan da Inter kowacce ta dauka sau 18.