Tottenham ta yi kunnen doki da West Brom

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tottenham ta barar da damar daukar kofin Premier bana

Tottenham ta tashi wasa kunnen doki 1-1 da West Brom a gasar cin kofin Premier wasan mako na 35 da suka fafata a ranar Litinin.

West Brom ce ta fara cin kanta, bayan da dan wasanta Dawson ya sa kai a kwallo ta shiga raga a minti na 33 da fara tamaula.

Dawson ne dai ya kuma farke kwallon da ya ci gida saura minti 17 a tashi daga fafatawar.

Da wannan sakamakon Leicester City wadda ke mataki na daya a kan teburin Premier ta bai wa Tottenham mai matsayi na biyu tazarar maki bakwai.

West Brom kuwa tana da maki 41 kuma daidai da na Everton da Watford da kuma Bournmouth.

Saura wasanni uku suka rage a kammala gasar, kuma Tottenham za ta ziyarci Stamford Bridge a ranar 2 ga watan Mayu.