Vardy ba zai buga karawa da Man United ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Saura wasanni uku suka rage a kammala gasar Premier bana

Jamie Vardy ba zai buga wasan da Leicester za ta yi da Manchester United ba a gasar Premier ranar Lahadi, sakamkon kara dakatar da shi wasa daya da aka yi.

A ranar 17 ga watan Afirilu aka bai wa Vardy jan kati a fafatawar da suka tashi 2-2 a wasan Premier da suka yi da West Ham.

Hakan ne ya sa dan kwallon bai buga wasan da Leicester ta ci Swansea 4-0 a gumurzun da suka yi ranar Lahadi, ba.

An kara hukuncin hana shi wasan ne da biyan tarar fam 10,000, saboda rashin da'a da ya nuna wa alkalin wasa Jon Moss, bayan da ya ba shi jan kati.

Ita ma Leicester City an ci tarar ta fam 20,000, saboda kasa tsawatarwa 'yan wasanta a lokacin da aka bai wa West Ham bugun fenariti a karawar.