Gasar Firimiyar Nigeria ta hada gwiwa da ta Laliga

Image caption Hukumomin biyu sun saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyar

Hukumar gudanar da gasar Firimiyar Nigeria ta sanya hannu kan yarjejeniya da ta La Ligar Spaniya domin yin aiki kafaɗa-da-kafaɗa.

Cikin yarjejeniyar da suka rattaba hannu da yammacin Talata a Abuja, hukumar gasar La Liga za ta taimakawa ta Nigeria da shawarwarin da za ta bunkasa tata gasar.

Haka kuma kungiyoyin kwallon kafa na kasashen biyu za su dinga buga wasan sada zumunta a tsakaninsu a filayen wasannin Nigeria da kuma na Spaniya.

Hukumar gasar La Liga za ta kuma bude ofishinta a Nigeria a cikin harabar ta Nigeria domin tuntubar junansu a fagen tamaula.

'Yan wasan Nigeria za kuma su samu saukin shiga kasar Spaniya, domin neman gurbin buga wa kungiyoyin Spaniya kwallon kafa.

An kammala buga wasannin mako na 13 a gasar Firimiyar Nigeria, yayin da ya rage saura karawa uku a kammala wasannin La Ligar bana.