Man City da Real Madrid sun tashi Canjaras

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Madrid za ta karbi bakuncin City a wasa na biyu ranar 4 ga watan Mayu

Manchester City ta tashi wasa canjaras babu ci da Real Madrid a wasan farko na gasar cin kofin zakarun Turai da suka yi a Ettihad a ranar Talata.

Real Madrid ta buga fafatawar ne ba tare da Cristiano Ronaldo ba, yayin da Yaya Toure bai buga wa City wasan ba, sakamakon jinya da suke yi.

Kafin wannan haduwar Manchester City ta kara da Real Madrid sau biyu a baya a gasar ta zakarun Turai, inda wasan farko Real Madrid ta ci City 3-2 ranar 18 ga watan Satumbar 2012.

Fafatawa ta biyu kuwa da suka yi a Ettihad, kungiyoyin biyu tashi wasa suka yi kunnen doki 1-1 a ranar Laraba 21 ga watan Nuwambar 2012.

Real Madrid za ta karbi bakuncin Manchester City a wasa na biyu a gasar bana a ranar Laraba 4 ga watan Mayu.