Sakho ba zai kalubalanci tuhumarsa ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Liverpool za ta kara da Villarreal a gasar cin kofin Europa

Mamadou Sakho ba zai kalubalanci sakamakon da ya nuna ya yi amfani da kwayoyi masu kara kuzari ba.

Ana kuma sa ran dan kwallon ba zai buga wa Liverpool wasannin da suka rage na gasar bana ba.

Ana binciken Sakho mai shekara 26 da laifin shan kwaya mai nau'in kona kitse, da aka gwada shi bayan da suka kara da Manchester United ranar 17 ga watan Maris a gasar Europa.

An bukaci da a sake gwada shi a ranar Talata karo na biyu, amma dan wasan bai amince da yin hakan ba.

Hukumar kwallon kafar Turai ba ta fara shirin zama domin daukar matakin ladabtarwa kan Sakhon ba.

Har yanzu Liverpool ba ta ce komai ba dangane da batun dan wasan.