Atletico Madrid ta ci Bayern Munich 1-0

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kungiyoyin za su sake karawa a ranar 3 ga watan Mayu a Jamus

Atletico Madrid ta ci Bayern Munich daya mai ban haushi a gasar cin kofin zakarun Turai wasan daf da na karshe ranar Laraba.

Atletico Madrid ta ci kwallon ne ta hannun Saul Niguez a minti na 11 da fara tamaula.

Kungiyoyin biyu sun taba karawa a gasar a shekarar 1974 a wasan karshe, inda a wasan farko ranar 15 ga watan Mayu a Brussels, suka tashi kunnen doki 1-1.

A wasa na biyu da suka yi a ranar 17 ga watan Mayu, Bayern Munich ce ta lashe kofin da ci 4-0.

Bayern Munich za ta karbi bakuncin Atletico Madrid a wasa na biyu ranar Talata 3 ga watan Mayu a Jamus.