Villarreal za ta fafata da Liverpool

Hakkin mallakar hoto reauters
Image caption Wannan ne karon farko da kungiyoyin biyu za su fafata

Liverpool za ta ziyarci Spaniya domin karawa da Villareal a gasar cin kofin zakarun Turai ta Europa a ranar Alhamis.

Kungiyoin za su fafata a gasar ce a wasan daf da na karshe, kuma wannan ne karon farko da za su kara a tsakaninsu.

Liverpool ta kai wasan daf da na karshe ne a gasar bayan da ta ci Borrusia Dortmund da ci 5-4 a fafatawa biyu da suka yi.

Ita kuwa Villarreal ta kai wannan matakin ne bayan da ta samu nasara a kan Sparta Prague da ci 6-3.

Haka ma Shakhtar Donetsk za ta karbi bakuncin Sevilla a wasan daf da na karshe a gasar.