Aston Villa: Agbonlahor ya bar muƙamin kyaftin

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kyaftin na Aston Villa, Gabriel Agbonlahor

Kyaftin ɗin Aston Villa, Gabriel Agbonlahor ya ajiye muƙaminsa na kyaftin a ƙUngiyar, ya kuma ƙara da neman afuwa kan halayyarsa a makonnin da suka gabata.

Aston Villa dai ta dakatar da dan wasan sakamakon hotonsa da aka dauka yana shagali, jim kadan bayan da kulob din ya silmiyo daga teburin Premier, a farkon watan nan.

Agbonlahor ya ce " Ban cancanci na cigaba da rike wannan matsayin ba."

Ya kara da cewa " Wannan matsayin abu ne mai alfarma a wurina kuma subucewarsa da ciwo."

Gabriel Agbonlahor ya kuma nemi afuwan magoya bayan Aston Villa a inda ya ce " Ina neman afuwar magoya bayan Aston Villa dangane da abin da ya faru."