Manajan Everton ya daura damarar yaki

Roberto Martinez Manajan Everton Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Roberto Martinez Manajan Everton

Manajan Everton Roberto Martinez yace a shirye yake ya fafata iya karfinsa yayin da ya ke ci gaba da fuskantar kakkausar adawa daga wasu magoya bayan kulob din.

Kungiyar kwallon kafar wadda ake yiwa lakabi da "The Toffes a turance" ta sami maki uku daga cikin maki 21 bayan da Manchester United ta doke ta a wasan kusa da na karshe na cin kofin FA na Ingila a ranar Asabar da ta wuce.

A wasannin da suka wuce magoya bayan kulob din sun rika daga kyallaye da tutoci su na kira ga manajan dan kasar Spain ya yi murabus.

An ambato shi yana cewa " Muna yiwa kanmu illa ne baki daya" Na san yadda suke ji. Kwallon kafa ba tare da shauki da kuma sha'awa ba, bai da amfani"

Martinez ya kara da cewa " A ko da yaushe ina karfafa gwiwar kyakkyawan zato da nasara mai daraja. Idan ba ka kasance a daya daga cikin wadannan ba to sai ka ga ana bin diddigi"

Sai dai kuma kaye da Kulob din ya sha da ci 4-0 a ranar 20 ga watan Aprilu a hannun Liverpool ya kasance babban koma baya ga burin manajan.

Everton dai ita ce ta 11 a jerin kulob kulob da ke gasar Premier, inda ta tsallake siratsin mayar da ita baya wato "relegation" da maki 10 yayinda suke da ragowar wasanni hudu da za su buga a nan gaba.