Pochettino zai tsawaita kwantiraginsa da Tottenham

Hakkin mallakar hoto no credit
Image caption Pochettino ya yi nasara kai kungiyar ta biyu a teburin Firimiya

Kociyan Tottenham Mauricio Pochettino ya ce yana shirin tsawaita kwantiraginsa da kulob din da shekara biyu har zuwa 2021.

Kocin dan kasar Ajantina, wanda ya jagoranci kungiyar har ta kai mataki na biyu a teburin Firimiya, an sha danganta shi da kokarin komawa Manchester United da Paris St-Germain.

Ya ce, "Mataki ne mai saukin dauka idan har kana da soyayyar mutane kuma kulob din yana da alamar tagomashi a gaba, don haka ban ga dalilin neman sauyi ba."

"Mun samar da sauyi sosai a fagen horo kuma ina ganinza mu cimma nasara nan gaba," in ji shi.

Pochettino mai shekara 44 ya koma Tottenham ne a watan Mayun 2014 bayan ya bar Southampton.