Arsenal na kara hawa teburin Premier

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan wasan Arsenal na murna

Kulob din Arsenal ne na uku a teburin gasar Premier da maki 67, bayan ya jefa kwallo daya mai ban haushi a ragar Norwich, a wasan da suka yi da yammacin Asabar.

Dan wasan Arsenal, Danny Wellbeck ne ya zura kwallon, bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Yanzu haka, akwai tazarar maki 8 tsakanin Arsenal din wadda ita ce mai matsayi na uku da kungiyar wasa ta West Ham wadda ita ce ta biyar.

Ita kuwa Norwich ta fado zuwa mai matsayi na 19 a teburin.