Leicester na gab da daukar kofi — Mata

Hakkin mallakar hoto
Image caption Juan Mata tare da kociya Luis Van Gaal

Dan wasan Manchester United na tsakiya, Juan Mata ya ce yunkurin da 'yan wasan Leicester suke yi na nuna cewa suna gab da lashe kofin gasar.

Idan dai Leicester ta doke Man United a wasan da za su yi ranar Lahadi, a Old Trafford, to za ta dauki kofin gasar Premier, a karon farko cikin shekaru 132 da kafuwa.

Mata ya ce " Suna nuna kwazo da jajircewa da kuma sha'awar kwallon."

Ya kara da cewa " A gaskiya suna gab da daukar kofi. Amma muna fatan hakan ba zai faru ba a filin wasa na Old Trafford. Fatana dai shi ne ganin mun dauki kofin."