Leicester: Da sauran rina a kaba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An ba wa dan wasan Leicester, Danny Drinkwater jan kati

Har yanzu, Leicester tana neman maki biyu ta lashe gasar Premier, bayan da suka tashi kunnen doki wato 1-1 da Manchester United, a Old Trafford.

Sai dai kuma Leicester za ta iya samun wannan dama, a ranar Litinin idan dai har kulob din Tottenham wanda shi ne na biyu, ya kasa doke Chelsea a Stamford Bridge.

Dan wasan Manchester United, Anthony Martial ne ya jefa kwallon farko, a ragar ta Leicester, kasa da minti 8 da fara wasa.

Sai dai kuma dan wasan Leicester, Wes Morgan ya farkewa kulob din nasa minti tara bayan nan.

Wasan dai bai yi wa dukkannin bangarorin dadi ba.Yayin da Leicester ba ta samu maki ukun da take nema ba domin samun damar kofi, ita kuwa Manchester United, wasan ya dakile mata kokarinta na cancantar samun gurbin shiga gasar zakarun turai.

Manchester United din dai tana mataki na biyar kuma akwai tazarar maki 4 tsakaninta da mai mataki na 4, wato Manchester City.