Swansea ta ci Liverpool 3-1

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Andre Ayew ne ya zura kwallaye biyu a ragar Liverpool.

Kungiyar wasa ta Swansea City ta samu gindin zama daram, a gasar Premier, bayan da ta ci Liverpool 3-1, a wasan da suka yi da yammacin Lahadi.

Dan wasan Swansea, Andrew Ayew ne ya zura kwallon farko da ta biyu a ragar Liverpool, a inda Jack Cork ya zarga ta uku.

Dan wasan Liverpool, Christian Benteke ya samu ya ceci kulob din nasa da jefa kwallo daya a ragar Swansea.

Yanzu haka, Swansea ta koma ta 13 a teburin gasar Premier kuma akwai tazarar maki 11 tsakaninta da Sunderland wadda ita ce ta uku daga kasan teburin gasar.

Ita kuwa Liverpool tana matsayinta na 7 a tebururin gasar da maki 55.