"Na tsammaci mummunan bore daga magoya baya"

Kociyan kungiyar kwallo ta Arsenal Arsene Wenger, ya ce ya yi zaton magoya bayan kulob din za su yi mummunan bore a wasan da suka yi ranar Asabar, inda suka ci Norwich 1-0.

Ya ce, "Na zaci za a lika fastoci ta ko ina a filin wasan. Ba wani buri da ya wuce ka sanya magoya bayanka farin ciki 100 bisa 100. Sai dai ban samu cimma wannan buri ba a wannan kakar wasan."

Nasarar da Arsenal ta samu a kan Manchester City ta sa kungiyar ta zama ta uku a teburin gasar Firimiya.

A watan Oktoba ne Mista Wenger, zai cika shekara 20 da jan ragamar kungiyar.