Ayew zai fuskanci binciken hukumar FA

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ayew ya ce bai ji dadin wani abu da aka fada ba a wurin zaman 'yan kallo na Sir Elton John.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta ce za ta yi bincike kan halayyar da dan wasan Aston Villa Jordan Ayew, ya nuna lokacin da wasan da kungiyarsa ta ci Watford 3-2 ranar Asabar.

Ana zargin Ayew da Idrissa Gana Gueye da shiga cikin wasu al'amura da suka shafi magoya bayan Watford.

Rahotanni sun ce dan wasan dan kasar Ghana mai shekara 24, ya haura allon tallace-tallace ya fuskanci 'yan kwallo tare da yin sa'insa da su.

An yi amanna cewa Ayew, wanda aka sauya shi a minti na 79, bai ji dadin wani abu da aka fada ba a wurin zaman 'yan kallo na Sir Elton John.