Uefa: Da wa Atletico Madrid za ta yi wasan karshe?

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dan wasan Atletico Madrid, Griezman

Kungiyar wasa ta Atletico Madrid ta doke Bayern Munich a zangon wasa na biyu na wasan kusa da karshe na gasar zakarun Turai, sakamakon tashin wasan da aka yi 2-2 a jumullar cin kwallaye.

Bayern Munich dai ta zura kwallaye biyu a ragar Atletico ta hannun Xabi Alonso da Robert Robert Lewandowski, a inda shi kuma Antoine Griezman ya ciwa kungiyar tasa kwallo daya.

Sakamakon zura kwallo daya mai ban haushi da Atletico ta yi a ragar Bayern Munich a zangon farko na wasan a lokacin da Bayern Munich ta je gidanta, ya sanya jumullar cin kwallaye tsakanin kungiyoyin ta zama 2-2.

Kuma kasancewar Bayern Munich a gidanta ake wasa, Atletico Madrid ta samu nasarar zuwa wasan karshe.

Yanzu haka, Atletico Madrid din za ta kara da Real Madrid ko Manchester City a wasan karshe.

Da yammacin Laraba ne dai Manchester City za ta fafata da Real Madrid, a gidanta.