Iyalai sun yi hijra saboda rigar Messi

Image caption Murtaza Ahmed sanye da rigar Messi ta kwaikwayo

Mahaifin yaron nan dan shekara biyar, wanda aka tallata a intanet sanye da rigar dan wasan Barcelona, Lionel Messi, ya ce iyalansu sun bar Afganistan saboda matsin lamba da suke samu.

An dai nuna Murtaza Ahmedi ne sanye da rigar Messi wadda ya kwaikwaya.

Kuma daga baya Lionel Messi ya aikowa Murtaza rigar tasa ta gaske.

Mahaifin yaron ya ce sakamakon irin tsangwama da kashedi da suke samu, yanzu haka sun yi kaura zuwa garin Quetta na Pakistan.