FA tana tuhumar Chelsea da Tottenham

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mousa Dembele lokacin da yake yakusar idon Diego Costa

Hukumar kwallon kafar Ingila wato FA tana tuhumar kungiyoyin Chelsea da na Tottenham a laifuka uku bisa kasa shawo kan 'yan wasansu da shugabanninsu lokacin wasan da suka yi ranar Litinin da ma bayansa.

Hukumar tana kuma tuhumar dan wasan tsakiya na Tottenham, Mousa Dembele da laifin nuna rashin da'a a lokacin wasan da suka tashi 2-2.

FA ta ce yakushin idon Diego Costa da Dembele ya yi, ba karamin laifi ba ne.

Idan dai har an same shi da laifin aikata hakan, to dakatarwar da za a yi masa ta fi ta wasanni uku.

Yanzu haka, an ba wa Dembele har zuwa ranar Alhamis da ya yi bayani kan abin da ya faru, a inda su kuma Chelsea da Tottenham aka ba su har zuwa ranar Litinin.

An dai raba yelon katina har guda 12 a lokacin wasan.