Darajar Leicester ta kai £200m

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption 'Yan wasan Leicester suna murna

Darajar kulob din Leicester City bayan lashe kofin gasar Premier za ta iya rubanyawa sau uku ko hudu, a kan kimar kudinta na farko.

An dai yi wa 'yan wasan kungiyar kudin goro a kan £57m, abin da ka nuni da cewa kungiyar ce ta fi kowacce araha a gasar Premier.

Wani mai lauyan harkokin wasanni, David Seligman ya ce "Jamie Vardy da Riyad Mahrez ne kawai darajarsu ta kai £70m." "Amma nan gaba darajar kulob din za ta kai £200m."

A 2012 ne Leicester ta sayi Jamie Vardy a kan £1m, a inda kuma aka sayi Riyadh Mahrez a kan £400,000, a 2014.