Verona: Luca Toni zai yi ritaya

Image caption Luka Toni yana bakin cikin rashin cin kwallo

Dan wasan gaba na kungiyar Verona, Luca Toni zai yi ritaya daga taka leda, bayan buga wasan da za su yi ranar Lahadi da Juventus.

Luca wanda yana cikin 'yan wasan da suka daukarwa Italiya kofin gasar kwallon duniya ta 2006, ta bugawa kungiyoyi takwas wasanni kuma ya zura kwallaye 156 a wasanni 343 na gasar La Liga.

Dan wasan, mai shekara 38, ya kasance wanda ya fi kowane dan wasa shekaru a lokacin da ya lashe kyautar dan wasan da ya fi kowa yawan kwallaye a gasar ta La Liga.

Bugu da kari, Toni ne dan wasan da ya fi kowa yawan kwallaye a gasar Bundesliga ta Jamus, a lokacin yana Bayern Munich, a 2007-2008.

Kuma a 2005-06, Luca ya lashe kyautar dan wasan da ya fi kowa zura kwallo a nahiyar Turai, bayan da ya ciwowa Fiorentina kwallaye 31.