Ba ma son sanannun 'yan wasa — Ranieri

Hakkin mallakar hoto PRESS ASSOCIATION
Image caption Jamie Vardy ne kawai kulob din ya saya a kan £1m

Kociyan Leicester City, Claudio Ranieri ya ce ba ya son kulob din ya shiga kwantaragi da 'yan wasan da suka yi suna.

Ya ce hakan zai yi barazana ga 'yan wasan kulob din da suka yi rawar gani wajen daukar kofin Premier a wannan kakar.

Ranieri ya dage cewa 'yan wasansa "na musamman ne."

An dai yi wa 'yan wasan Leicester kudin goro a kan £57m, abin da ke nuni da cewa kungiyar ce ta fi kowacce araha a gasar Premier.