'Yan wasa sun fara barin Newcastle

Hakkin mallakar hoto skysport
Image caption Daya daga cikin 'yan wasan da zai bar Newcastle, Sylvain Marveaux

'Yan wasan Newcastle United na gefe, Gabriel Obertan da Sylvain Marveaux, sun bar kulob din.

Kulob din dai ya yarda da tafiyar 'yan wasan tun kafin kwantaraginsu ta kare domin su samu wata kwantaragin da wata kungiyar.

Obertan, mai shekara 27, ya koma Newcastle ne daga Manchester United a 2011 kuma ya ci wa kulob din kwallaye uku a wasanni 77.

Shi kuma Marveaux, mai shekara 30, ya je kulob din ne daga Rennes.