Za mu yi amfani da damarmu kan Sevilla — Klopp

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Klopp ya ce za su yi bakin kokarinsu.

Kociyan Liverpool Jurgen Klopp ya ce kulob din zai yi amfani da "damarsa" a lokacin da za su fafata da Sevilla a wasan karshe na cin kofin Europa ranar 18 ga watan Mayu.

Kulob din ya casa Villareal da ci 3-1 ranar Alhamis, ko da ya ke kafin nan sai da Villareal ya doke shi da ci 1-0 a zagayen farko na wasan dab da na kusa da karshe.

Klopp ya ce, "Idan muka murza leda kamar yadda muka yi a baya, to lallai za mu yi zarra, kuma abin da muke shirin yi kenan. Za mu je gidansu, sannan mu yi bakin kokarinmu."

Wasan - wanda za su yi a filin St Jakob-Park na Basel da ke kasar Switzerland - shi ne zai kasance karon farko da Liverpool zai kai zagayen karshe na cin kofin nahiyar Turai tun bayan da suka sha kaye a hannun AC Milan da ci 2-1 a gasar Zakarun Turai ta shekarar 2007.

Liverpool ya yi nasara a wasan karshe takwas cikin 11 da suka buga a Turai - biyar daga cikin bakwai na cin kofin Zakarun Turai, sannan uku cikin hudu na cin kofin Uefa da Europa.

Idan suka doke Sevilla, wadanda ke son daukar kofin Europa sau uku a jere, za su bi sahun Sevilla wajen zama wadanda suka fi yin nasara a gasar, inda za su dauki kofi hudu, lamarin da zai sa su samu gurbi a gasar cin kofin Zakarun Turai.