Oxlade-Chamberlain ba zai buga Euro 2016 ba

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An yi tsammanin Oxlade-Chamberlain zai buga wasan da rukunin 'yan kasa da shekara 21 na kulob din Arsenal suka yi a farkon wannan makon.

Dan wasan Ingila da Arsenal Alex Oxlade-Chamberlain ba zai buga gasar cin Kofin Turai ta shekarar 2016 ba sakamakon jinyar da yake yi ta gwiwarsa.

Kociyan Arsenal Arsene Wenger ya ce dan wasan, mai shekara 22, zai ci gaba da jinya zuwa makonni shida ko takwas.

Oxlade-Chamberlain ya ji rauni a gwiwarsa ne a wasan da kulob din Barcelona ya doke su a gasar cin kofin Zakarun Turai ranar 23 ga watan Fabrairu.

Wenger ya kara da cewa "Babu wata dama a gare shi ta buga gasar kofin Turai. Zai dawo murza leda ne a farkon watan Yuni."

An yi tsammanin Oxlade-Chamberlain, wanda ya fara murza wa Ingila leda a wasan da ta doke Norway a shekarar 2012, zai buga wasan da 'yan kasa da shekara 21 na kulob din Arsenal suka yi a farkon wannan makon.