An ci tarar Pillars sama da naira miliyan 2

Hakkin mallakar hoto Kano Pillars Web Site
Image caption Enyimba ce ta samu nasara a kan Pillars da ci 2-1 a filin wasa na Sani Abacha da ke kofar mata, Kano

Hukumar gudanar da gasar Firimiyar Nigeria ta ci tarar Kano Pillars kudi naira miliyan biyu da dubu dari hudu, sakamakon nuna halin rashin da'a da magoya bayanta suka yi.

Hukumar ta samu magoya bayan Pillars da laifin jefa abubuwa cikin fili dama shiga filin a kwantan wasan gasar da Pillars ta yi rashin nasara a hannun Enyimba da ci 2-1 a ranar Laraba.

Pillars din za ta biya naira 500,000 na jefa abubuwa da shiga filin wasa, za kuma ta biya jami'an Enyimba naira 250,000 domin yi wa wadanda suka ji rauni magani.

Haka kuma Enyimba za ta karbi naira 150,000 kudin gyaran motarta da aka lalata bayan da aka tashi daga fafatawar.

Hukumar ta gasar Firimiya za kuma ta saka ido a kan Pillars din sosai, ta kuma ja kunnenta idan aka sake samun irin haka za ta buga wasanni biyu a gida babu 'yan kallo.