Middlesbrough ta samu tikitin shiga Premier

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shekara bakwai rabon kungiyar da buga gasar Premier

Middlesbrough ta samu tikitin shiga gasar Premier da za a yi ta badi, bayan da ta tashi kunnen doki 1-1 da Brighton & Hove Albion.

Cristhian Stuani ne ya fara ci wa Middlesbrough kwallo a minti na 19 da fara tamaula, kuma bayan da aka dawo daga hutu ne Dale Stephens ya farkewa Brighton kwallon da aka ci ta.

Sai dai kuma Brighton ta kammala karawar da 'yan wasa 10 a cikin filin, bayan da aka bai wa Dale Stephens jan kati a fafatawar.

Middlesbrough wadda rabonta da gasar Premier shekara bakwai baya, za ta buga gasar badi ne tare da Burnley wadda ta lashe kofin Championship.

Kungiyoyi hudu ne za su fafata domin neman gurbi daya da ya rage na shiga gasar Premier badi da suka hada da Brighton da Hull City da Derby da kuma Sheffield Wednesday.