Manchester United ta ci Norwich City 1-0

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Norwich da Man United kowaccensu na da kwantan wasa daya

Damar Norwich City ta ci gaba da buga gasar cin kofin Premier ta badi na kara dusashewa, bayan da Man United ta doke ta da ci daya mai ban haushi.

Manchester United ta ci kwallonta ne ta hannun Mata a wasan gasar mako na 37 da suka fafata a filin wasa da ke kan titin Carrow a ranar Asabar.

Da wannan sakamakon Norwich City tana mataki na 19 da maki 31, za kuma ta fafata da Watford a gida kafin ta ziyarci Everton a wasan karshe.

United kuwa tana mataki na biyar a kan teburi da maki 63, za kuma ta ziyarci West Ham sannan ta karbi bakuncin Bournemouth.