Ekeng ya mutu bayan da ya fadi a filin wasa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Patrick Ekeng dan kwallon tawagar Kamaru

Dan wasan Dinamo Bucharest, Patrick Ekeng, ya mutu bayan da ya fadi a cikin filin wasa a lokacin da yake yi wa kungiyarsa tamaula.

Ekeng dan kasar Kamaru mai shekara 26, ya mutu ne a minti na 70 inda ake nuna karawa a talabijin tsakanin Dinamo da Viitorul a gasar cin kofin Romania.

Ana zargin cewar dan kwallon ya gamu da ciwon zuciya ne a lokacin da yake tsaka da wasa, kuma awanni biyu da kai shi asibiti, likitoci suka bayar da sanarwar mutuwar tasa.

Hukumar kwallon kafa ta Romania ta dakatar da dukkan wasannin da za a buga na wannan mako.

A ranar Juma'a hukumar kwallon kafa ta Kamaru ta bayar da sanarwar mutuwar Ekeng a shafinta na sada zumunta na Twitter.

Ekeng kafin mutuwarsa ya buga wa kulob din Le Mans da kuma Lausanne wasanni.

A shekarar 2003 Marc-Vivien Foe ya mutu bayan da ya fadi a cikin fili a lokacin gasar Confederation tsakanin Kamaru da Colombia a Faransa.