Sunderland ta doke Chelsea da ci 3-2

Image caption Sunderland za ta buga da Everton a ranar Laraba

Sunderland ta doke Chelsea da ci 3-2 a gasar Premier wasan mako na 37 da suka kara a ranar Asabar.

Diego Costa ne ya fara ci wa Chelsea kwallon a minti na 14 da fara wasa, Khazri ne ya farkewa Sunderland kwallo, sai dai kuma Matic ya kara ci wa Chelsea kwallo na biyu.

Bayan da aka dawo daga hutu ne Borini ya farkewa Sunderland kwallo, sannan kuma Defeo ya ci wa Sunderland ta uku kuma ta 15 da ya ci a gasar bana.

Sunderland ta koma mataki na 17 da maki 35 a teburin Premier, za kuma ta karbi bakuncin Everton a ranar Laraba, kafin ta ziyarci Stoke City a wasan karshe a gasar ta Premier.

Ga sakamakon wasu wasannin da aka yi a ranar Asabar:
  • Norwich City 0 : 1 Manchester United
  • Aston Villa 0 : 0 Newcastle United
  • West Ham United 1 : 4 Swansea City
  • Crystal Palace 2 : 1 Stoke City
  • Bournemouth 1 : 1 West Bromwich Albion