Za a koma buga kofin zakarun Turai a karshen mako

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Barcelona ce ke rike da kofin bara, an kuma fitar da ita daga gasar bana

Za a fara buga wasannin gasar cin kofin zakarun Turai a karshen mako daga shekarar 2021.

Hakan dai daya ne daga cikin shawarwarin da hukumar kwallon kafa ta Turai ta tattauna kan kara martaba gasar, da samun karin mabiya wasannin kungiyoyin nahiyar.

Sai nan da shekara biyar ne za a fara yin wasannin gasar a karshen mako, saboda yarjejeniyar da hukumar ta kulla ta nuna wasannin a talabijin a baya.

An fara buga wasannin gasar cin kofin zakarun Turai da a baya ake kira da European Cup a cikin tsakiyar mako tun a shekarar 1968.

Sai dai kuma idan aka dawo yin wasannin gasar a karshen mako za a yi la'akari da lokutan gasar wasannin kasashen hukumar da ake nunawa a talabijin.