An yi canjaras tsakanin dan Kirisfo da Jimama

Image caption Karawa uku suka yi a damben babu kisa alkalin wasa shagon Amadi ya raba su

An yi wasanni goma a damben gargajiya da aka fafata da safiyar Lahadi a gidan damben Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja Nigeria.

A cikin wasannin guda daya ne aka yi kisa, shi ne wanda Bahagon Dan Kirisfo daga Arewa ya buge Garkuwan Bahagon Dan Kanawa daga Kudu a turmi na biyu.

Sa zare da aka yi tsakanin Audu Dan Kirisfo daga Arewa da Shagon Jimama daga Kudu ta kayatar, inda suka dunga yin amarya a kowanne turmi ukun da suka yi babu kisa.

Ga sauran wasannin da aka dambata babu kisa:
  • Garkuwan Autan Faya daga Kudu da Shagon Shukurana daga Arewa
  • Alin Tarara daga Arewa da Abbati daga Kudu
  • Shagon Buzu daga Arewa da Dan Daba Autan Sikido daga Kudu
  • Garkuwan Shagon Mada daga Kudu da Fijo daga Arewa
  • Shukurana daga Arewa da Bahagon Dan Kanawa daga Kudu
  • Shagon Faya daga Kudu da Shagaon Abban Na Bacirawa daga Arewa
  • Dan Aliyu Langa-Langa daga Arewa da Matawallen Kwarkwada daga Kudu
  • Dan Aminu Langa-Langa daga Arewa da Dogon Minista daga Kudu